Connect with us

News

KAROTA ta cafke ɓarawo bayan ya saci wayoyi 6 da turarruka a rana ɗaya

Published

on

FB IMG 1645647256761
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

A jiya Talata ne dai Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano, KAROTA ta cafke wani ƙasurgumin ɓarawo, mai suna Lawan Khalid, wanda ya ƙware gurin shiga shaguna ya yi sata.

Hukumar, ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a, Nabilusi Abubakar Ƙofar-Na’isa, ta ce ta samu nasarar kame ɓarawon ne bayan da ta samu bayanan sirri da ga masu shaguna daban-daban waɗanda ya yi wa sata.

A cewar Ƙofar-Na’isa, ɓarawon na yin sata ne ta hanyar ɗaukar shatar babur ɗin adaidaita-sahu ya na kai shi shaguna daban-daban a cikin birnin Kano ya na sace musu wayoyi da kayaiyaki.

Advertisement

Ya ƙara da cewa da ya shiga hannu, wanda a ke zargin, Lawan, ya ce aikin ƙwaya ne duk ya janyo halin da ya tsinci kan sa.

A cewar sa, ƙwayar da ya ke sha ne da sauran kayan maye su ke zuga shi ya na aikata wannan laifi, inda ya nuna mafakar ruwa ba zai sake yi ba.

Ƙofar-Na’isa ya ƙara da cewa Hukumar ta KAROTA za ta miƙa shi Lawan ɗin ga hannun ƴan sanda domin yi ma sa hukuncin da ya dace.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *