News
Majalisar Dokokin Zamfara ta tabbatar da Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna
Daga kabiru basiru fulatan
Awanni kaɗan bayan tsige Mahdi Aliyu Gusau, Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta tantance Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna.
Nasiha shine Sanata mai ci da ke wakailtar Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattijai.
Ƴan majalisar sun tabbatar da Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna a wata ƙuri’a ta bai-ɗaya.
Gwamnan Jihar, Bello Matawalle, a wata wasiƙa danya rubuta wa Sakataren Gwamnati, Kabiru Balarabe sannan Kakakin Majalisar, Nasiru Magarya ya karanta a zaman majalisar na yau Laraba, ya miƙa sunan Nasiha a matsayin sabon Mataimakin Gwamna bayan cire Mahdi Aliyu.
Sai Shugaban Masu Rinjaye, Faruku Dosara ya miƙa ƙudurin tabbatar da Nasiha, wanda dukka mambobin su ka amince.
Kakakin Majalisar ya baiyana cewa naɗin sabon Mataimakin Gwamnan ya yi daidai da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999.
-
News3 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News1 day ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News2 days ago
Gwamnatin Kano Ta Ayyana 1 Ga Satumba A Matsayin Ranar Hutun Bikin Takutaha
