Connect with us

News

Yanzu -yanzu: Majalisar dokokin Zamfara ta tsige mataimakin gwamnan jihar

Published

on

1645629072509
Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

 

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara a ranar Laraba ta kaɗa ƙuri’a domin tsige mataimakin gwamnan jihar Barrista Mahdi Aliyu Gusau.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan majalisa 20 cikin 24 sun zaɓi a tsige mataimakin gwamnan bayan wani rahoto da kwamitin shari’a a jihar ya gabatar a kansa da ya same shi laifi kan zarge-zargen da ake yi masa.

Advertisement

Ɗaya daga cikin ƴan majalisar da suka halarci zaman Honarabul Ibrahim Tudu Tukur mai wakiltar Bakura ya tabbatar wa BBC da cewa su 21 cikin 24 suka halarci zaman kuma mutum 20 sun amince da a tsige mataimakin gwamnan.

Tsigewar ta biyo bayan amincewa da rahoton da wani kwamitin bincike da ya binciki zarge-zargen da ake yi wa mataimakin gwamnan na saba ka’idar aiki ya mika.

Mataimakin gwamnan ya yi zargin cewa an yi masa bi-ta-da-kulli ne saboda ya ki sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tare da gwamnan jihar.

Advertisement

A wata hira da ya taba yi da BBC mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi Aliyu Gusau ya ce gwamna Matawalle bai nemi shawararsa ba har zuwa lokacin da ya yi wanka zuwa jam’iyyar APC.

Daga cikin dalilan da majalisar ta bayyana na tsige mataimakin gwamnan sun haɗa da rashin amsa gayyatar da aka yi masa ba, batun da Mahdi Aliyu Gusau ya ce an saɓa doka wajen bin ka’idar tsige shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi.

Honorabul Faruk Musa Dosara shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar ya kuma shaida wa BB cewa: “Dama a baya an gabatar da tuhumar da ake yi wa shi mataimakin gwamna ga babbar mai shari’a ta jihar Zamfara.

Advertisement

Ko da yake an gabatar da wannan rahoto na kwamitin kudi na jihar Zamfara, sai aka kafa kwamitin lauyoyi masu zaman kansu da ba su da alaƙa da gwamnati ko siyasa. Bayan an rantsar da su sun ci gaba da aikinsu.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *