News
Sauron Da Jirgi Ya Dauko Daga Afirka Sun Yi Ajalin Mutane 2 A Jamus
Mutane biyu da ke aiki a filin jirgin saman Frankfurt da ke Jamus sun mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro (malaria), bayan da ake zargin sauro mai ɗauke da cutar ya shigo ƙasar a cikin wani jirgin sama daga yankin da malaria ta zama ruwan dare.
Hukumomin lafiya sun ce jimillar ma’aikatan filin jirgin guda shida ne suka kamu da cutar, yayin da mutane huɗu ke samun kulawa.
Gwamnatin Ghana Ta Yi Watsi Da Tallafin Cedi Miliyan 20 Daga Kamfanin MTN
Cibiyar Kula da Cututtuka da Rigakafi ta Jamus, Robert Koch Institute (RKI), ta ce ana kyautata zaton cewa wata sauro daga jinsin Anopheles mai ɗauke da ƙwayar malaria ce ta shigo filin jirgin ta cikin jirgin sama, inda daga bisani ta ciji ma’aikatan.
A cewar RKI, ma’aikatan da abin ya shafa sun kamu da rashin lafiyar ne a tsakanin 4 zuwa 6 ga Yuli 2026, duk da cewa ba su yi tafiya zuwa ƙasashen da malaria ta zama ruwan dare ba.
Hukumar lafiya ta Frankfurt ta kuma jaddada cewa babu wata alama da ke nuna cewa cutar na yaɗuwa daga mutum zuwa mutum a wannan lamari.
A yanzu haka, an kafa tarkunan kama sauro a filin jirgin domin gano nau’in sauro da kuma tushensa. Haka kuma, ana gudanar da bincike kan sauro da aka kama domin gano inda ya fito.
