News
Kotu ta bada umarnin ƙwace kadarori 10 a Abuja da Kaduna da kuma wasu kuɗaɗe a Amurka ma su alaƙa da Yari
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori 10 da kudade a bankuna na wucin-gadi, da a ke zargin na tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ne.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Mai shari’a Obiora Egwuatu ya bada wannan umarni ne a ranar Laraba ya yin da ya ke yanke hukunci kan karar da lauyan ICPC, Osuobeni Ekoi-Akponimisingha ya gabatar.
Egwuatu ya ce umurnin na wucin gadi da aka bayar zai dauki tsawon kwanaki 60 don baiwa hukumar ICPC damar kammala binciken ta, daga nan ne hukumar za ta iya neman a kwace kadarorin na dindindin.
Alkalin ya umurci ICPC da ta bayyana wannan umarni ga duk wani mutum ko masu sha’awar kadarorin na da kwanaki 14 don a nuna cewa kotu ta na da ikon ƙwace kadarorin na dindindin.
A cewa ICPC, wasu da ga cikin kadarorin na Maryland da ke Amurka, Abuja, Kaduna da sauran gurare.l