News
A yayin da Rasha ta mamaye Ukraine, Koriya ta harba makami mai linzami akalla guda daya, a matsayin gwaji

Daga kabiru basiru fulatan
Hafsan hafsoshin sojojin Koriya ta Kudu sun sanar da cewa, Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami da ke gabashin gabar tekun Koriya a ranar Lahadi.
An harba makamin daga yankin Sunan na Koriya ta Arewa da misalin karfe 7.52 na safe agogon kasar, in ji rundunar hadin gwiwa.
Ministan tsaron Japan Nobuo Kishi ya ce Koriya ta Arewa ta harba “aƙalla makami mai linzami guda ɗaya”, wanda ya yi tafiya mai nisan kilomita 300 (mil 186) kuma ya kai tsayin kilomita 600 (mil 373), in ji CNN.
Kwamitin tsaron kasar Koriya ta Kudu (NSC) ya ce harba makamin ba abu ne da ake so ba don tabbatar da zaman lafiya yayin da duniya ke kokarin warware yakin Ukraine, a cewar fadar Blue House, ofishin shugaban kasar Koriya ta Kudu.
NSC ta kuma nuna matukar damuwa da nadama matuka dangane da harba makami mai linzami karo na takwas a bana, sannan ta bukaci Arewa da ta gaggauta dakatar da ayyukan da suka sabawa sulhu ta hanyar diflomasiyya.
Koriya ta Arewa ta kara kaimi wajen gwajin makami mai linzami a shekarar 2022, inda ta sanar da shirin karfafa garkuwarta”. a cewar kafofin yada labaran kasar.
DAILY TRUE HAUSA ta ruwaito cewa A cikin makonni hudun farko na shekarar 2022 kadai, Koriya ta Arewa ta kaddamar da gwaje-gwajen harba makami mai linzami guda bakwai, amma babu daya daga cikin makamanta masu cin dogon zango.
Manazarta sun ce karin gwajin da aka yi a bana ya nuna cewa Kim yana kokarin cimma burin cikin gida da kuma nuna wa duniya da ke kara tabarbarewa cewa Pyongyang karanta yakai tsaiko
“Pyongyang tana da kyakkyawan tsari na soji. Karfin gwamnatin Kim da sahihancinsa na da nasaba da gwada harba makamai masu linzami.”