News
Gwamnatin Kano na shirin gudanar da auren zawarawa — Kwamishiniya
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad ta baiyana cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa wajen gudanar da shirin nan ba da daɗewa ba.
Ta kuma baiyana cewa Insha Allahu shirin zai gudana ne ta hanyar ma’aikatar kula da mata, inda ta ƙara da cewa kuma za ta zaɓi marayu da marasa galihu a sanya su a cikin shirin.
Dakta Zahra’u ta baiyana hakan ne a wata sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labaran Ma’aikatar, Bahijja Malam Kabara ta fitar a yau Lahadi.
Sanarwar ta ce Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a yayin wani taron daurin aure na mutane 31 maza da mata, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a yau Lahadi.
A cewar ta, matsalar tattalin arziki, sakamakon annobar korona na ɗaya da ga cikin manyan ƙalubalen da su ka sanya a ka samu tsaiko a shirin auren zawarawa da ƴan mata da Gwamnatin Kano ta saba yi.
Daga nan sai ta yi kira ga ma’aurata da su yi biyayya ga juna, kuma su bi ka’idojin aure kamar yadda ya ke a Musulunci.
Kwamishiniyar ta kuma yaba da ƙoƙarin Gidauniyar FOMWAN da DARUL ARQAM da su ka shirya taron, ta re da yin kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan kyakkyawan misali.