News
Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10. Sun Yi Garkuwa Da Wasu A Jihar Kaduna

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Akalla mutane goma ne da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kashe a wasu hare-hare daban-daban a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Hakazalika, ‘Yan ta’addan sunyi garkuwa da wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba, musamman mata, a yayin samamen da ya dauki tsawon sa’o’i da dama.