Connect with us

News

Kenya: Jam’iyya Mai Mulki Tana Goyon Bayan Dantakaran Jam’iyyar Adawa A Zaben Shugaban Kasa

Published

on

FB IMG 1645938500183
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

 

 

Advertisement

 

Jam’iyya mai mulki a kasar Kenya ‘Jubillee Party’ ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar jam’iyyar adawa Raila Odinga, wanda yake shiga takarar shugabancin kasar karo na 4.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa shugaba Uhuru Kenyata ya ce jam’iyyarsa tana goyon bayan Odinga dan shekara 77 a duniya ne, don yayi imani da iya shugabanci duk da cewa shi ba dan jam’iyyarsa ba.

Advertisement

Hakan na faruwa ne a dai-dai lokacinda mataimakin shugaban kasa William Ruto ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a karkashin wata sabuwar jim’iyya da ya kafa, mai suna ‘United Democratic Alliance’.

Uhuru kenyata dai baya daga cikin wadanda zasu tsaya takarar shugabncin kasar wanda za’a gudanar a cikin watan Augusta mai zuwa, don ya cika shekaru biyar-biyar har sau biyu, wanda kundin tsarin mulkin kasar ya amince masa.

Odinga ya tsaya takarar shugabancin kasar Kenya a shekara 2007, 2013, da kuma 2017, inda aka yi rikicin kabilancin bayan zabubbuka na shekara ta 2007 da kuma ta shekara ya 2017. mutane da dama sun rasa rayukansu a rikice-rikicen. Kenyata, Odinga da kuma Ruto duk suna wakiltan maya-manyan kabilun kasar ta Kenya wadanda suke jujjuya iko a tsakninsu tun bayan samun ‘yencin kan kasar a shekara ta 1963 daga hannun turawan Ingila.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *