Connect with us

News

Mutum 91 sun kamu, 21 sun mutu a cikin mako daya a Najeriya

Published

on

Screenshot 20220227 061510
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

Hukumar NCDC ta bayyana cewa a cikin mako na bakwai na shekarar 2022 wato daga 14 zuwa 21 ga Fabrairu, mutum 91 sun kamu da zazzabin lassa kuma cutar ta yi ajalin mutum 21 a kasar nan.

Alkaluman da hukumar ta gabatar ranar Juma’ar da ta gabata ya nuna cewa adadin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya karu daga mutum 77 zuwa mutum 91.

An gano yaduwar cutar a jihohin Edo, Delta, Ebonyi, Enugu, Taraba, Bauchi, Gombe, Kogi, Nasarawa da Ondo.

Advertisement

Hukumar ta ce duk da haka adadin yawan mutanen da cutar ta kashe bai kai yawan mutanen da cutar ta kashe a watan Fabrairun 2021 ba.

A jimla mutum 450 ne suka kamu da cutar a kananan hukumomi 74 dake jihohi 21 na kasar nan.

Cutar ya fi tsanani a jihohin Ondo, Edo da Bauchi.

Advertisement

Abubuwan da za a kiyaye don gujewa kamuwa da Zazzabin Lassa

1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.

2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.

Advertisement

3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.

4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.

Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.

Advertisement

5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.

6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.

7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.

Advertisement

8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.

9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.

10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.

Advertisement

11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *