News
Haryanzu Kwankwaso na nan a PDP-Bashir Sanata
Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
Sakataren yada labaran jami’iyyar PDP a nan Kano Bashir Sanata ya musanta labaran da ke cewa tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin ficewa daga jami’iyyar.
Bashir Sanata ya bayyana haka ne a zantawarsa da INDARANKA
Ya ce, labarin da wasu jaridu a kasar nan ke ci gaba da ya dawa sam babu kanshin gaskiya a ciki, domin kuwa lokaci ne kawai zai fayyace ko Kwankwason zai ci gaba da zama a PDP ko kuma zai fice daga jami’iyyar.
“Zan iya cewa wasu jaridu ne da suke so a ce sune suka fara yada labarin, wanda kuma babu kanshin gaskiya a ciki ko kadan,” a inji Bashir Sanata.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da rahotanni ke bayyana Sanata Kwankwaso na shirin ficewa daga jami’iyyar PDP zuwa jami’iyyar NNPP a kasar nan.