Connect with us

News

Makaman nukiliya nawa Rasha ta mallaka?

Published

on

1646219822785
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin

Shugaba Vladmir Putin ya bayar da umarnin ɗana makaman Nukiliyar Rasha, abun da ya tayar da hankalin duniya.

To sai dai masu sharhi na ganin cewa matakin wani yunƙuri ne na nunawa ƙasashen duniya yatsa, da su kauce wa shiga yaƙin da ya ƙaddamar a Ukraine, ba wai yana son amfani da su ba.

Advertisement

Makaman Nukiliya dai sun kasance a duniya tun kusan shekaru 80 da suka gabata, kuma ƙasashe da dama na kallonsu a matsayin wata kariya ga harkokin tsaronsu.

Makaman Nukiliya nawa Rasha ke da su?

Ana da ƙididdigar yawan makaman Nukiliya a duniya baki ɗaya, to amma a cewar kungiyar masana kimiyya ta Amurka, Rasha na da makaman Nukiliya 5,977, ko da yake lokacin amfanin 1,500 daga cikinsu ya ƙare, kuma nan gaba kaɗan za a lalata su.

4500 daga cikinsu da suka rage sun kasance masu zubin makaman roka da rokoki, waɗanda ka iya yin tafiya mai nisan zango.

Advertisement

Ragowar kuwa ƙanana ne, waɗanda tasirinsu ba ya haifar da mummunar ɓarna, kuma ana amfani da su ne a fagen daga, ko ta cikin ruwa.

Wannan ba wai yana nufin cewa Rasha na da makaman Nukiliya masu yawa ba ne da za a iya harbawa nan take.

Masana sun yi ƙiyasin cewa an girke 1,500 daga cikinsu, a wuraren harba makamai masu linzami da sauran wuraren harba makamai.

Advertisement

Ya kwatankwacinsu yake da na sauran ƙasashe?

Bayan Rasha, akwai sauran ƙasashen duniya guda takwas da suka mallaki, makaman Nukiliya, sun haɗar da China da Faransa, da India da Isra’ila da Koriya Ta Arewa, da Pakistan, da Amurka da Burtaniya.

Ƙasashen China da Faransa da Rasha da Amurka da Burtaniya da wasu ƙasashen duniya 191 sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman da ake kira NPT.

A ƙarkashin yarjejeniyar dole ne su rage yawan makaman nasu, kuma sun nuna za su aiwatar da hakan.

Advertisement

An yi imanin cewa yarjejeniyar ta janyo rage yawan makaman tun daga shekarun 1970 zuwa yanzu.

Ƙasashen Indiya da Isra’ila da Pakistan ba za su taɓa shiga yarjejeniyar ba, yayin da ita kuwa Koriya Ta Arewa ta shuri takalmanta ta fice a shekarar 2003.

Isra’ila ce ɗaya tilo cikin dukkan waɗannan ƙasashe da har yanzu ta ƙi shelantawa duniya cewa tana da Nukiliya, amma ƙasashen duniya sun yi imanin tana da su.

Ukraine ba ta da Nukiliya, sannan duk da zargin da shugaba Putin ke yi mata, har yanzu ba ta da wata hujja da ke tabbatar da zargin cewa tana da shi.

Advertisement
line

Wacce irin ɓarna Nukiliya ke yi?

An ƙera makaman Nukiliya ne don haifar da gagarumar ɓarna.

Girman ɓarnar da za su iya yi ya danganta da wasu abubuwa da dama, kamar:.

  • Girman makamin
  • Nisan inda aka harba shi
  • Wurin da aka harbawa

To sai dai hatta su kansu ƙananan makaman Nukiliyar na iya haifar da babbar ɓarna, musamman asarar rayuka da kuma illata muhalli tsawon shekaru.

Bam din da ya kashe mutane kusan 146,000 a Hiroshima na kasar Japan lokacin yakin duniya na biyu ya kai nauyin kiloton 15.

Kuma makaman nukiliya irin na wannan zamanin na iya yin nauyin kiloton 1,000.

Advertisement

Ana kyautata zaton cewa mutane ƙalilan ne za su iya tsira a duk inda aka harba Nukiliya.

Sharhi daga Gordon Corera

Wakilin BBC kan sha’anin tsaro

Ya kamata hankalinmu ya tashi? Gaskiya ne a baya-bayan nan hankula sun tashi a kan maganar Nukiliya, amma a iya cewa yanzu lamura sun dan lafa.

Advertisement

Ko da umarnin Putin barazana ce ba wai shirin amfani da su ba, a iya cewa lissafi na iya ƙwacewa wani ɓangare musamman idan aka kasa fahimtar juna.

Sakataren tsaron Birtaniya Ben Wallace ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu Birtaniya ba ta ga wani sauyi a ainihin yanayin makaman nukiliya na Rasha ba.

Za a sanya ido sosai kan hakan, kamar yadda majiyoyin leken asiri suka tabbatar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *