News
Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Haaland, Broja, Rudiger, Saka, Werner da Lewandowski
Ana ganin Arsenal za ta kyautata wa ɗan wasan gaban Ingila Bukayo Saka mai shekara 20 ta hanyar tsawaitawa da kuma inganta kwantiraginsa a ƙarshen wannan kaka. (football.london)
Manchester City ta tattauna da wakilin ɗan wasan gaban Borussia Dortmund mai shekara 21 Erling Braut Haaland. (Fabrizio Romano, via Express)
Dortmund ba ta cire rai dangane da ci gaba da ajiye Haaland a wurinta ba a ƙarshen kaka duk da ita ma Barcelona na hararar ɗan wasan. (Mirror)
Akwai yiwuwar Chelsea ta sayar da ɗan wasan gaban Albania Armando Broja mai shekara 20 da kuma ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 20 Faustino Anjorin domin amfani da kuɗinsu wajen sayen ‘ƴan wasa a wannan kakar. (Evening Standard)
Wakilan ɗan wasan bayan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger mai shekara 28 na ci gaba da tattaunawa da Real Madrid da PSG. (Sky Sports)
Akwai yiwuwar mamallakin Chelsea Roman Abramovich zai iya sayar da ƙungiyar inda ake sa ran a cikin makon nan za a soma tayi. (Telegraph)
Ɗan wasan tsakiyar Arsenal kuma ɗan ƙasar Faransa Matteo Guendouzi zai koma Marseille a matsayin aro kan wata yarjejeniya ta din-din-din ta fam miliyan 9 a ƙarshen wannan kaka. (RMC Sport, via Mirror)
Daraktan ƙwallon ƙafa John Murtough ya ce ana bin ƙa’ida matuƙa wajen ganin an samu kocin Manchester United na gaba. (Manchester Evening News)
Borussia Dortmund na son sayen ɗan wasan Chelsea mai shekara 25 Timo Werner. (Sky Germany)
Har yanzu ɗan wasan gaban Bayern Munich ɗan ƙasar Poland Robert Lewandowski mai shekara 33 bai yanke shawara ba kan makomarsa inda ya ce a shirye yake ya rungumi kowacce irin ƙaddara. (Sky Sports Germany, via 90min)
Barcelona ta ƙagara ta sayi ɗan wasan Monaco mai shekara 22 Aurelien Tchouameni. (Sport – in Spanish)
Tsohon ɗan wasan gaban Sifaniya Diego Costa mai shekara 33 na daf da komawa kulob ɗin nan na Brazil wato Corinthians. (Star)
Tsohon golan Liverpool David James na ganin cewa golan nan na Ireland Caoimhin Kelleher mai shekara 23 zai bar Anfield domin nemo wa kansa suna a wani wuri. (Mirror)