News
Za mu sasanta da Sarkin Kano sabo da mutum ne mai son zaman lafiya — Air Peace

Daga muslim yunus abdullahi
Shugaban kamfanin jirgin sama na Air Peace, Allen Onyema ya baiyana cewa hukumomin kamfanin za su ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, nan ba da daɗewa ba don tattaunawa kan abinda ya faru.
A makon da ya gabata ne a ka ɗan samu rashin jituwa tsakanin fadar Sarkin Kano da Kamfanin na Air Peace a yayin dawowar Sarkin zuwa Kano da ga tafiyar da ya yi zuwa wasu ƙasashe na Afirka.
Sai dai kuma Onyeama ya bayyana cewa ba zai bari wannan rashin fahimta ya tada ƙura ba sabo da ya san Sarkin Kano mutum ne mai son zaman lafiya.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugabannin kamfanin jaridar Daily Independent.
“Ban san wannan abun ya tada hazo haka ba kuma ba na so Kamfanin Air Peace ya zama musababbin tada hatsaniya a kasar nan.
“Na kasance mutum mai son zaman lafiya. Tun lokacin da na ke da ƙananan shekaru. Don haka zan yi abun da ya dace domin kashe wannan wutar.
“Saboda haka ba zan bari ayi amfani da ni wajen raba ƙasar nan ba. Na daɗe da sanin Sarkin Kano tun yana Ciroma, lokacin da mahaifinsa ke da rai.
“Zamu haɗu wata rana, na san ba mutum ne mai son rigima ba kuma ina da tabbacin zai so ya haɗu da ni kuma nima ina son haɗuwar da shi.” in ji Onyeama
A cewar Onyema, babu wata matsalar da wannan saɓanin zai haifar.