Connect with us

News

Matan da ake zargin mazajensu da taimaka wa Boko Haram na zanga-zanga a Kano

Published

on

FB IMG 1646227947830
Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

Kano

Hukumomi a ƙasar na zargin mazajen nasu ne da taimaka wa ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta Boko Haram ta hanyar yi musu canjin kuɗin ƙasar waje.

Kano

Mafi yawan mazajen da ake tsare da su fiye da shekara ɗaya ‘yan kasuwar canji ne da aka fi sani da wapa, kuma tun da aka kama su ba a bari iyalansu sun gan su ba in ban da kwanan nan, a cewar matan.

Kano

Matan ƙarƙashin jagorancin Aisha Jibril sun ce “buƙatarmu ita ce a gurfanar da su a gaban kotu, masu laifi a hukunta su, waɗanda ba su da laifi a sako mana mazajenmu”.

Kano

Wasu daga cikin matan sun fito ne tare da ‘ya’yansu ƙanana maza da mata.

A 2021 ne wata kotu a Dubai da ke ƙasar Daular Larabawa (UAE) ta yanke wa wasu ‘yan Najeriya hukunci, ciki har da ɗaurin rai-da-rai, saboda kama su da laifin yi wa Boko Haram canjin kuɗaɗe.

Sakamakon haka ne jami’an tsaro a Najeriya suka fara kamen wasu ‘yan canjin da ake zargi da tallafa wa ƙungiyar wajen yi musu safarar kuɗaɗe.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *