News
MATSALAR MAI: PDP ta yi Allah wadai da Buhari kan yawan tafiye-tafiye da watsi da ƴan Najeriya

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda tafiya kasar waje da kuma watsi da ‘yan Najeriya a cikin karancin man fetur a fadin kasar.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun National Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar, Hon. Debo Ologunagba.
Jam’iyyar ta zargi shugabannin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) dake jagorantar al’amuran da suka shafi harkar man fetur na gurgunta harkokin tattalin arziki a Najeriya.
“Shawarar da shugaban ya yanke
Muhammadu Buhari na tafiya Kasar Ingila don sake duba lafiyarsa na yau da kullun bayan da gwamnatinsa ta lalata mana tsarin kiwon lafiyarmu da kuma lokacin da al’ummar da yake jagoranta suka shiga cikin mawuyacin hali.
“Yayin da sauran shugabannin duniya ke magance matsalolin kasashensu, shugaban kasa Buhari, wanda ya yi alkawarin gyara mana harkokin mai, ya yi watsi da ‘yan Nijeriya da muguwar matsalar man fetur da cin hanci da rashawa da ‘yan APC ke tafkawa a harkokin tattalin arzikin man fetur a kasar nan.”
“Saboda cin hanci da rashawa da watsi da aiki da jam’iyyar APC ke yi, al’ummarmu a halin yanzu ta shiga cikin halin kaka-ni-kayi na ‘yan kasuwa, inda tuni suka yi wa ‘yan Najeriya farashi na Naira 500 kan kowace litar man fetur, lamarin da ya janyo tashin gwauron zabi na sufuri. , farashin abinci, magunguna, da sauran muhimman kayayyaki”