Sports
Rasha zata buga World Cup ko kuma a fasa gasar gabaki daya – Putin ya gargadi FIFA

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Da yake mayar da martani ga manema labarai a birnin Moscow kan matakin da FIFA ta dauka na haramtawa kasar Rasha daga duk wasu harkokin wasanni.
Putin yace “Dukkansu munafukai ne kuma ko kadan ban damu ba saboda kwallon kafa da siyasa ba sa haduwa”.
“FIFA kada ta kuskura ta yi hakan idan ba haka ba tun farko ba za a yi gasar cin kofin duniya ba’.