Connect with us

Sports

Qatar 2022: Najeriya ta bayyana ‘yan wasanta da za su fafata da Ghana

Published

on

1646458335033
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta bayyana kashin farko na ‘yan wasan da za su buga mata fafatawa da Ghana a wasan neman cancantar shiga Kofin Duniya na Qatar 2022.

Matashin ɗan wasan gaba na Leicester City Ademola Lookman na cikin tawagar, inda zai saka wa ƙasarsa riga a karon farko.

Advertisement

A kwanan nan ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Fifa ta bai wa Lookman damar buga wa Najeriya wasa bayan fara saka wa Ingila riga.

Kazalika, tawagar ta ‘yan ƙwallo 32 ta ƙunshi matashi Akinkunmi Amoo, wanda ya wakilci ƙasar a gasar Kofin Duniya na ‘yan ƙasa da shekara 17.

a fara buga wasan ne a ranar 25 ga watan Maris a Ghana kafin a buga wasa na biyu a Najeriya a 29 ga wata da zimmar fitar da wadda za halarci gasar da ƙasar Qatar za ta karɓi baƙunci karon farko a tarihinta.

Advertisement

Sauran taurarin da ke cikin tawagar sun haɗa da kyaftin Ahmad Musa, da William Ekong, da Wilfred Ndidi, da Moses Simon, da Kelechi Iheanacho.

Cikakkiyar tawagar

Tawagar Super Eagles
Masu tsaron raga

Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, Afirka ta Kudu); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands).

‘Yan wasan baya

Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, Ingila); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Spain); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); William Ekong (Watford FC, Ingila); Olaoluwa Aina (Torino FC, Italiya); Calvin Bassey (Glasgow Rangers, Scotland); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal).

Advertisement

‘Yan wasan tsakiya

Frank Onyeka (Brentford FC, Ingila); Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland); Wilfred Ndidi (Leicester City, Ingila); Oghenekaro Etebo (Watford FC, Ingila); Akinkunmi Amoo (FC Copenhagen, Denmark).

‘Yan wasan gaba

Advertisement

Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkiyya); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Spain); Victor Osimhen (Napoli FC, Italiya); Moses Simon (FC Nantes, Faransa); Sadiq Umar (UD Almeria, Spain); Odion Jude Ighalo (Al-Hilal FC, Saudiyya); Kelechi Iheanacho (Leicester City, Ingila); Emmanuel Dennis (Watford FC, Ingila); Ademola Lookman (Leicester City, Ingila).

‘Yan benci

Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkiyya); Jamilu Collins (SC Padeborn 07, Jamus); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Rasha); Taiwo Awoniyi (Union Berlin, Jamus); Paul Onuachu (KRC Genk, Belgium); Peter Olayinka (SK Slavia Praha, Czech Republic); Ogenyi Onazi (Al-Adalah FC, Saudiyya)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *