News
Zelensky: Ba buya nake yi ba. Kuma ba tsoro nake ji ba

Daga Muhammad Muhammad Zahraddin
A cikin daren jiya shugaban kasar Ukraine ya wallafa wani bidiyo cikin wadanda yake wallafawa a kullum. Sai dai a wannan karon ya wallafa shi ne daga ofishin shugaban kasa da ke birnin Kyiv.
Ya ce ba boyewa yake yi ba. Kuma ya ce ba ya tsoron makomarksa.
Ana ganin bayyana wurin da yake ga duniya sako ne ga Vladimir Putin – domin har yanzu dakarun ukraine na kare birnin Kyiv daga harin da Rasha ke kai wa kan babban birnin kasar na Ukraine.