News
Ba Za Mu Bude Jami’o’in Najeriya Ba, Har Sai An Cika Mana Alkawuran Da Aka Yi Mana Tun Na Shekarar 2009, Inji ASUU
Daga yasir sani abdullahi
A jiya Litinin, 7 ga watan Maris 2022, Ministan ilmin Najeriya, Adamu Adamu ya ba kwamitin da ya kafa wa’adin watanni uku ya gama aikinsa na cika alkawuran da gwamnati ta yiwa kungiyar malaman jami’o’in kasar da ma’aikatan jami’o’in.
Nauyin da ke kan wannan kwamiti shi ne duba yarjejeniyar da gwamnatin kasar ta shiga da kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT a shekarar 2009.
Shugabannin kungiyar malaman jami’a watau ASUU sun nuna ba za su dawo aiki ba sai an cika alkawuran nan, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Wannan kwamiti mai mutane bakwai zai yi aiki ne a karkashin Nimi Briggs. Wannan labari bai yi wa ASUU dadi ba, ta ce ba za ta yarda da wannan shirin ba.
-
News18 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
