Connect with us

News

Akanta Janar Zai Gurfana Gaban Majalisa Kan Ware Wa Hukumar Bogi Naira Biliyan 1.32 A Kasafin 2026

Published

on

Majalisar Wakilan Tarayya (1)

Akanta Janar na Ƙasa, Shamseldeen Ogunjimi, zai gurfana a gaban Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai a yau Litinin domin yin bayani kan yadda aka ware wa wata hukuma da ake zargin ba ta wanzuwa fiye da Naira biliyan 1.32 a cikin Kasafin Kuɗin Tarayya na shekarar 2026.

Kwamitin, wanda Hon. Yusuf Gagdi, mai wakiltar mazaɓar Kanke/Kanam/Pankshin ta Jihar Filato ke jagoranta, na gudanar da bincike kan yadda aka saka Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) cikin kasafin kuɗi, duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba ta san da kafuwar irin wannan hukuma ba.

Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadiyyar mutuwar Mutane 107 Tare Da Jikkata 344 A Pakistan

Ana sa ran zaman sauraron bayanan zai mayar da hankali kan yadda aka shigar da kuɗaɗen wannan hukuma cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, tare da gano mutanen da suka taka rawa wajen aiwatar da lamarin.

Kwamitin ya ce binciken na da nufin tabbatar da gaskiya, kare dukiyar al’umma da kuma tabbatar da cewa ana gudanar da harkokin kasafin kuɗi cikin gaskiya da rikon amana.

Idan aka tabbatar da zargin, ana sa ran binciken zai iya haifar da ɗaukar matakan doka kan duk wanda aka samu da hannu wajen ware wa hukumar da ba ta da sahihancin wanzuwa wannan kuɗi mai yawa.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending