News
Ruwan Sama Mai Karfi Ya Rusa Gidaje Sama Da 300 A Katsina
Ruwan sama mai ƙarfi tare da iska ya haddasa mummunar barna a garin Dangamau da ke ƙaramar hukumar Kusada ta Jihar Katsina, inda gidaje sama da 300, shaguna da sauran kadarori na miliyoyin naira suka rushe.
Lamarin ya jefa ɗaruruwan mazauna yankin cikin matsanancin hali, bayan da iyalai da dama suka rasa matsugunansu tare da lalacewar dukiyoyinsu.
Akanta Janar Zai Gurfana Gaban Majalisa Kan Ware Wa Hukumar Bogi Naira Biliyan 1.32 A Kasafin 2026
Hukumomin Jihar Katsina sun tabbatar da faruwar iftila’in, inda suka bayyana cewa ruwan sama mai ƙarfi haɗe da iska sun haddasa asarar dukiyoyi masu yawa tare da kawo cikas ga rayuwar al’ummar yankin.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jajanta wa al’ummar Dangamau da sauran waɗanda bala’in ya shafa, yana mai cewa gwamnati ta damu matuƙa da irin asarar da aka yi.
Gwamnan ya ce rasa gidaje da kadarori ya jefa iyalai da dama cikin ƙunci, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ba su duk tallafin da ya dace domin rage musu radadin wannan ibtila’i.
A cewarsa, tuni ya umarci hukumomin da abin ya shafa su gudanar da cikakken bincike da tantance irin barnar da aka yi, domin fara kai agajin gaggawa ga waɗanda iftila’in ya rutsa da su.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta fara shirye-shiryen kai kayan agaji, da suka haɗa da abinci, matsuguni na wucin gadi da sauran kayan buƙata ga iyalan da abin ya shafa.
Gwamna Radda ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an agaji haɗin kai yayin da ake ci gaba da aiwatar da matakan tallafa wa waɗanda bala’in ya shafa.
A halin da ake ciki, wannan iftila’i na daga cikin jerin bala’o’in damina da jihar Katsina ke fuskanta a bana.
A makon da ya gabata, ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar wasu ‘yan uwa biyu, Muhammad Salisu mai shekara 12 da Abdurrahman Salisu mai shekara bakwai, a unguwar Janbango da ke cikin birnin Katsina, bayan ruwan sama ya kwashe su yayin da suke dawowa daga makarantar Islamiyya.
Mazauna yankin Janbango sun sake kira ga gwamnatin jihar da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta gina ingantattun magudanan ruwa da ɗaukar matakan kariya daga ambaliya, domin dakile asarar rayuka da dukiyoyi a lokutan damina.
