News
Ƴan Kwankwasiyya sun kai wa Shekarau ziyarar tuntuɓa a Abuja

Daga kabiru basiru fulatan
Wasu jiga-jigai a Kwankwasiyya, ɗariƙar siyasar da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta, sun kai wa Sanata Ibrahim Shekarau ziyarar tuntuɓa a gidan sa da ke Abuja a jiya Alhamis.
Alamu dai sun nuna cewa wasu da ga cikin mabiya darikar Kwankwasiyya ɗin za su yi tutsu na kin bin jagoran nasu zuwa jam’iyar NNPP kamar yadda a ke raɗe-raɗi.
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa, waɗanda su ka ziyarci Shekarau, wanda shi ne jagoran ɓangaren G7 a APC, sun haɗa da Yusuf Bello Danbatta, Abubakar Nuhu Danburam da Zainab Audu Bako.
Rahotanni sun bayyana cewa, sun ziyarci Sanata Shekarau, mai wakailtar Kano ta tsakiya, a gidansa domin zawarcinsa zuwa jam’iyyar PDP.
Duk da ba a san mai su ka tattauna a tsakanin su ba, amma kakakin Shekarau ɗin, Sule Ya’u Sule, ya tabbatar da cewa ƴan Kwankwasiyya sun ziyarci mai gidan nasa.
“A jiya ne ‘ya’yan kungiyar Kwankwasiyya ta PD, karkashin jagorancin tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Danburan su ka kai ziyarar tuntuba ga mai girma Sanata Ibrahim Shekarau a gidansa da ke Abuja,” in ji Sule.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun bayan da Kwankwaso ya sanar da yiwuwar sauya sheƙa zuwa NNPP, sai jita-jita ta kunno kai cewa Shekarau zai dawo jam’iyar sa ta PDP, bayan da shi ma ya yi rashin nasara a hannun Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a kotun ɗaukaka ƙara, kan rikicin shugabancin APC a Kano.