Sports
Kasuwar ƴan ƙwallon: Makomar Lukaku, Lewandowski, Zanilo, Eriksen, Pochetino da Zidane
Daga maryam bashir musa
Chelsea ta shirya kyale dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku ya bar kungiyar a kakar wasa ta bana, inda Inter Milan da Paris St-Germain ke zawarcin dan wasan mai shekaru 28. (90Minutes)
Manchester United ta sanya farashin £40m kan golan Ingila Dean Henderson, mai shekara 25, wanda ke da sha’awar barin Old Trafford a bazarar nan, kuma Newcastle na cikin wadanda ake zawarcinsa. (Star)
Kocin Manchester United Erik ten Hag zai kawo mataimakinsa Mitchell van der Gaag zuwa Old Trafford amma Robin van Persie bai yanke shawarar komawa kungiyar ba.(Mirror)
Manchester City ta kara tattaunawa kan batun neman dan wasan gaban Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 21.(Star).
Real Madrid ta yi yunkurin daukar Haaland daga kungiyar ta Premier amma a makare (Sports Spanish)
Roma na tunanin barin dan wasan tsakiyar Italiya Nicolo Zaniolo ya tafi a karshen kakar wasa ta bana kuma za ta yi tunanin sanya farashinsa a kan kusan Yuro miliyan 60, yayin da tuni kungiyoyin Serie A da Premier League ke zawarcinsa. (Corriere dello Sport)
Kungiyar Braga ta Portugal tana son tsohon dan wasan Juventus Andrea Pirlo, mai shekara 42, ya zama kocinta a kakar wasa mai zuwa. (A Bola – in Portuuese)
Liverpool na zawarcin dan wasan baya na Aberdeen dan kasar Scotland Calvin (Sun)
Dan wasan Brentford dan kasar Jamus Vitaly Janelt, mai shekara 23, ya ce ya tuntubi kungiyoyin Premier da na Bundesliga kan yuwuwar tafiya bayan ya taka rawar gani a Bees a kakar wasa ta bana.(Kicker)
Paris Saint-Germain a shirye take ta raba gari da Mauricio Pochettino kuma tana fatan ta nada Zinedine Zidane a matsayin sabon kocinta. (Le Parisien)
Dan wasan gaba na Bayern Munich dan kasar Poland Robert Lewandowski na ba wa Barcelona da ke fatan daukarsa wahala, kasancewa dole ne ta salami wasu ‘yan wasa da dama domin samun damar daukasa (Sports Spanish)
Barcelona ta dawo kan gaba wajen sayen dan wasan gaban Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 24, daga Inter Milan, inda kulub din na Italiya ke Shirin sauya matsaya a kan farashin da ya sanya na farko idan za a hada masa da wani dan wasa a yarjejeniyar. (Marcha)
Crystal Palace da Tottenham na shirin fafatawa a neman dan wasan bayan Peterborough na Ingila Ronnie Edwards, mai shekara 19, kan fan miliyan 15.(Mail)
Tsohon dan wasan baya na Newcastle Jose Enrique ya yi imanin dan wasan kasar Denmark Christian Eriksen zai zama babban dan wasa a kungiyar idan dan wasan mai shekaru 30 ya bar Brentford a karshen kwantiraginsa na kankanin lokaci. (Chronicle)
