Connect with us

News

Siyasar Kano: Dauda lawan ya ajiye muƙaminsa don takarar ɗan majalisa

Published

on

Daga muhammad Muhammad zahraddin

 

 

 

Babban mai taimakawa Gwamnan Kano kan ci gaban al’uma Ahmad Dauda Lawan ya ajiye muƙaminsa domin tsayawa takara a zaɓen 2023.

A wata sanarwa da ya fitar, Ahmad Dauda ya ce, ya sauka daga muƙamin ne domin biyayya ga sabuwar dokar zaɓe.

Advertisement

Dauda Lawan ya ce, yana neman ɗan majalisar jihar mai wakiltar ƙaramar hukumar Tarauni.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Gwamna Ganduje ya bai wa masu riƙe da muƙaman siyasa da ke sha’awar takara umarnin ajiye aiki domin biyayya ga dokar zaɓe.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending