News
Ƴan sanda sun kama mutum da ɗauri 250 na wiwi a Kano Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano a jiya Asabar ta kama wani matashi mai shekaru 33 da haihuwa, mai suna Agbo Victor da ke fataucin miyagun kwayoyi, ɗauke da ɗauri 250 na tabar wiwi. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Kano. Ya ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake tafiya a cikin wata mota makare da yanar wiwin a Kwanar Dangora a Ƙaramar Hukumar Kiru ta jihar. HlKiyawa, ya ce wanda ake zargin ya dauko kayan ne daga Edo zuwa wani dillalin miyagun kwayoyi da ke Kano, wanda yanzu haka ya tsere. Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Samaila Shuaibu Dikko, ya bayar da umarnin mika shi zuwa sashin binciken miyagun kwayoyi na sashin binciken manyan manyan laifuka na rundunar domin bincike mai zurfi. Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.
Daga Yasir sani Abdullahi
Ƴan sanda sun kama wani mutum da ɗauri 250 na wiwi a Kano
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano a jiya Asabar ta kama wani matashi mai shekaru 33 da haihuwa, mai suna Agbo Victor da ke fataucin miyagun kwayoyi, ɗauke da ɗauri 250 na tabar wiwi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a Kano.
Ya ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake tafiya a cikin wata mota makare da yanar wiwin a Kwanar Dangora a Ƙaramar Hukumar Kiru ta jihar.
HlKiyawa, ya ce wanda ake zargin ya dauko kayan ne daga Edo zuwa wani dillalin miyagun kwayoyi da ke Kano, wanda yanzu haka ya tsere.
Ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Samaila Shuaibu Dikko, ya bayar da umarnin mika shi zuwa sashin binciken miyagun kwayoyi na sashin binciken manyan manyan laifuka na rundunar domin bincike mai zurfi.
Kakakin ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan an kammala bincike.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
