News
Hajj 2022: Maniyyata sun koka a kan tsadar kuɗin aikin hajji bana a Najeriya
Daga Hamza Yusuf Abdulmumin
Maniyatta aikin hajjin bana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan sanarwar da hukumar alhazai ta kasa a Najeriya ta fitar kan kudin aikin hajjin.
Duk da cewa an rika hasashen cewa kudin hajjin bana zai karu sakamakom matsin tattalin arziki da tsadar dala amma maniyyata ba su yi tunanin cewa al’amarim zai kasance haka ba.
A ranar Alhamis ne Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya wato NAHCON ta bayanna cewa za a kara kudin aikin hajji da akalla kashi 50 cikin 100 kan abin da maniyyata suka biya a 2019.
Hukumar ta yi hasashen cewa kudin aikin hajjin bana ba zai gaza naira miliyan biyu da rabi ba.
NAHCON ta alakanta ƙaruwar farashin da yanayin tattalin arziƙi da kuma hauhawar farashin dala, sai dai wasu maniyata na cewa ya kamata gwamnati ta yi duba na tsanaki kan lamarin.
Wani maniyyaci ya shaidawa BBC cewa kusan shekara biyu kenan da biyan kudinsa, amma karin ba zai hana shi neman hanyoyin samun ciko domin kamala biya kudin aikin hajjin.
“Gwiwata ba ta yi sanyi ba. Shi abu ne na hukuncin ubangiji. Idan Allah ya yi kiran ka toh za ka amsa kiransa kuma cikin hukuncin ubangiji za mu tafi nema mu ga mai Allah zai yi mana,”In ji shi.
Sai dai ya yi kira ga gwamnati a kan ta taimaka wa talakawan da ke son su je kasa mai tsarki.
“Mun ajiye kudin nan kusan shekara biyu a hannun gwamnati, toh ya kamata a ce an duba an tausaya, ta san mai za ta yi ta agazawa wannan aikin hajji da aka shafe shekara biyu ba a yi ba.”
Ita ma wata mata waddake burin sauke farali ta shaidawa BBC cewa hankalinta ya matukar tashi da jin labarin karin kudin saboda kudin da ta biya a baya da kyar ta hada su.
“Gaskiya na ji kamar ba zan iya ba saboda tun lokacin da sakon ya same ni, gaba daya duk tunani na ya rikice, ina ta tunanin ya ya ma zan yi na samun cikon wannan kudin.”
Suma kamfanonin shirye shiryen tafiye-tafiyen aikin hajji da ummarah duk sun sun koka da karuwar farashin kujerun aikin hajjin.
Hukumomin Saudiyya sun ware wa Najeruya kujeru fiye da dubu 40 cikin maniyyata miliyan daya da ta ce zata amince su gudanar da aikin Hajjin bana.
Kafar yada labaran kasar ta ruwaito mahukuntan kasar na cewa dole mahajjatan da za su je aikin Hajjin na bana su kasance ‘yan kasa da shekara 65, kuma dole sai an yi musu rigakafin korona cikakke.
A shekarar da ta wuce ‘yan kasar dubu 60 ne kadai suka yi aikin Hajjin.
A shekarun baya kafin bullar korona Musulmi daga sassan duniya kusan miliyan biyu da rabi ne ke aikin Hajjin.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
