News
Sojojin Najeriya sun kwace bindigogi fiye da 500 a hannun fararen hula
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa ta kwace bindigogi marasa lasisi fiye da 500 daga hannun fararen hula a jihar Filato da ke tsakiyar kasar.
Bindigogin wadanda yawansu ya kai 517, ciki har da wasu samfuri AK-47 da kanana da kuma wadanda aka kera a gida sun shiga hannun rundunar ne yayin wani biki da aka gudanar a birnin Jos a jiya Alhamis.
An dai kwato su ne daga hannu masu aikata laifuka, cikinsu ma akwai ‘yan fashi da makami da mambobin kungiyoyi masu satar mutane suna garkuwa da su domin kudin fansa, kamar yadda wani kakakin rundunar ya shaiida wa BBC.
An kuma kwace wasu bindigogin ne a jihohin Kaduna da Bauchi masu makwabtaka da jihar ta Filato, sannan an kama wasu mutanen da aka samu dauke da makaman.
A shekarar da ta gabata, wani kiyasi na cewa akwai akalla bindigogi miliyan shida da rabi a hannun jama’ar Najeriya – kuma kashi 90 cikin 100 na hannun wadanda ba hukumomi ne ba.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
