News
Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun saki hotunan mutane 40 da suka sace.
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Yan bindiga sun saki hotunan mutane 40 da suka sace a Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna watan Maris Cikin hotuna biyu akwai mata ashirin da uku (23) da kuma maza goma sha bakwa (17) zaune kan leda Da alamun yan bindigan na bibiyan kafafen yada labarai saboda wannan karon sun rufe bayansu
Wata guda cir bayan harin da yan bindiga suka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna inda akalla mutum 9 suka hallaka, yan ta’addan sun saki hotunan fasinjojin dake hannunsu. Wata Lakcara a jami’ar jihar Kaduna, Bilkisu Yero, ce ta saki hotunan a shafinta an Facebook. Hotunan da aka saki ranar Litinin ne karo na uku yan bindigan zasu saki bidiyo ko hoto dake nuna cewa wadanda suka sace na raya cikin lafiya. Har yanzu, gwamnatin Najeriya ta gaza fadin takamammen adadin mutanen da aka sace.
Wata daya kenan suna rike da fasinjojin kuma mutum daya kadai, Alwan Hassan, suka saki bayan ya biya kudi N100m.
Harin jirgin kasa Abuja-Kaduna: Yan bindiga sun saki hotunan mutanen da suka sace
A cikin daya daga cikin hotunan, akwai mutum 23, yawanci mata da yara. 3 Yan bindigan sun leda a kasa yayinda suka rufe bayansu da zanin gado. A cikin hoto na biyu kuwa, akwai maza 17 zaune cikin sahu.
Legit ta samu ji daga bakin wani mazaunin Zaria, Muhammad Malumfashi, cewa daya daga cikin wadanda ke cikin hotunan sunansa Sadiq Ango Abdullahi, dan siyasa ne kuma mai niyyar takaran kujerar dan majalisar wakilai. Wani ma’aikacin gwamnati, Yusuf Atta,a Facebook yace: “Wayyo yar uwata da mahaifiyata. Sune na farko da ta biyu daga dama zaune a kasa. Allah ya fida ku baki daya.”
Habiba AbdulAziz kuwa tace: “Wayyo Allah, ga mahaifiyata da yar uwata. Allah ya fiddasu daga wajen wadannan mutanen.” Wani Isma’el Yarima kuwa yace: “Ga yar uwata ca. Allah ya kare ku.”
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
