News
ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA: Ƴan kwana-kwana sun ceto zakara da ya faɗa rijiya a Kano
Daga mujahid danlami Garba
Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da ceto wani zakara mai shekara ɗaya da ya faɗa rijiya a jihar.
Kakakin Hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a unguwar Ƙwalli, cikin birnin Kano a yau Talata.
Ya ce hukumar, da misalin ƙarfe 10:12 na safe ta samu kiran gaggawa be da ga wani mai suna Kamalu Garba, cewa an samu faɗawa rijiya.
Kakakin ya ƙara da cewa a daidai ƙarfe 10:15, sai jami’an hukumar su ka isa wajen da haɗarin ya faru, inda su ka tarar cewa wani zakara ne ya faɗa cikin rijiya.
Abdullahi ya ce tuni jami’an hukumar su ka ceto shekararren zakaran da ran sa, inda a cewar Kakakin, an kai shi sashin gaggawa na asibitin dabbobi na jihar domin kula wa da lafiyar sa.
Abdullahi ya ce tuni a ka sallami zakaran kuma ya dawo gida cikin koshin lafiya.
Wasu mazauna unguwar dai sun ce zakaran ya faɗa rijiyar ne yayin da ya ke yin cara don burge wata kaza, ai kuwa, a cewar mazauna unguwar, bai aune ba sai jin shi ya yi a cikin rijiya.
-
News7 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News6 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News5 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
