Connect with us

News

Bayan Ya Tsayar Da Gawuna, Ganduje Zai Sayi Fom Din Takarar Sanata Mai Wakiltar Arewacin Kano

Published

on

Daga yasir sani Abdullahi 

 

Advertisement

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya shirya tsaf domin siyan fom din takarar kujerar sanata mai wakiltar arewacin Kano a yau Litinin.

Advertisement

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, Ganduje ya yanke wannan hukuncin ne a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda suka yi a sirrance a gidan gwamnati.

Wata majiya mai dauke da labarin daga taron, ta ce Gwamnan zai siya fom din a yau Litinin.

Advertisement

Hakan na nuni da cewa, Ganduje ya shirya tsaf domin fatattakar Sanata Barau Jibrin wanda yanzu haka yake rike da kujerar.

Duk da cewa, Jibrin ya bayyana cewa zai nemi takarar gwamna, amma har yanzu bai siya fom din ba.

Advertisement

Kafin yanzu, Jibrin na hannun daman Ganduje ne kuma ana kallonsa a matsayin wanda Ganduje zai zaba domin gadar kujerarsa kafin ruwa ya yi tsami tsakaninsu kuma ya koma tsagin APC na G7 wanda Sanata Ibrahim Shekarau yake shugabanta.

Hakan na zuwa bayan da Gwamna Ganduje ya zabi Dr Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda zai gane shi a kujerar gwamna.

Advertisement

Ganduje, wanda zai sauka daga madafun iko a watan Mayun shekara mai zuwa bayan maimaita kujerarsa, dan asalin karamar hukumar Dawakin Tofa ne, wacce ke yankin arewacin jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending