News
Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Mbappe, Griezmann, Perisic, De Jong, Bellingham
Daga mujahid danlami Garba
Real Madrid na da kwarin guiwa fiye da a ko wane lokaci cewa za ta cimma aniyarta ta dauko Kylian Mbappe, sai dai kuma har yanzu dan wasan na PSG da Faransa bai yanke shawara kan makomarsa ba. (Fabrizio Romano)
Barcelona ba da ta da sha’awar Antoine Griezmann, mai shekara 31, ya koma kungiyar daga aron da ta bayar da shi ga Atletico Madrid, idan har Atleticon ba za ta ci gaba da rike shi ba. Dan wasan da Barcan ke so a yanzu na farko shi ne Robert Lewandowski. (Cuatro – in Spanish)
Sai dai kuma shugaban Bayern Munich Herbert Hainer ya ce Lewandowski yana da yarjejeniyar zama a kungiyar tasa ta Jamus har zuwa watan Yuni na 2023 kuma dan wasan na Poland mai shekara 33 zai cika wannan yarjejeniya. (Sport Buzzer – in German)
Chelsea ta cimma yarjejeniya ta farko kan cewa za ta dauki dan wasan gaba na gefe na Crotia, Ivan Perisic, mai shekara 33, wanda kwantiraginsa zai kare da Inter Milan. (Mediaset, via Metro)
Bisa ga dukkan alamu dan wasan tsakiya na Barcelona da Holland Frenkie de Jong, mai shekara 25, zai ki amsa goron gayyatar tafiya Manchester United, yayin da sabon kocin United da zai kama aiki Erik ten Hag, ya kuduri aniyar tsaurara mataki a kan ‘yan wasan da ke son barin Old Trafford a bazaran nan. (Star)
Matashin dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekara 18, ya kawar da jita-jitar da ake yi ta cewa zai tafi Manchester United ko Liverpool, inda ya tabbatar cewa zai taka wa Borussia Dortmund leda ne a kaka mai zuwa. (Mirror)
Swansea City na fuskantar hamayya daga sabbin kungiyoyi biyu da suka tsallaka zuwa gasar Premier, Fulham da Bournemouth, a zawarcin dan wasan tsakiya dan Wales, Joe Allen mai shekara 32, daga Stoke City. (Wales Online)
Romelu Lukaku, ya ce ba zai sake barin wani mutum yayi magana a madadinsa ba bayan da wakilinsa Federico Pastorello, ya yi hira da wata jaridar Italiya kan yuwuwar sake komawarsa Italiya. (Star)
Rahotanni na cewa wakilin dan wasan gaba na Juventus da Argentina Paulo Dybala, mai shekara 28, yana London, domin duba bukatar da kungiyoyin Premier ciki har da Arsenal ke yi wa dan wasan. (Calciomercato via Football Italia)
West Ham za ta hakura da sha’awar da take yi wa dan bayan Burnley dan Ingila James Tarkowski, mai shekara 29, saboda kungiyar, na sa ran zai tafi Newcastle a bazaran nan. (Mirror)
