Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Salah, Mane, Kounde, Ekitike, Pogba, De Jong, Keita, Palhinha
Daga Maryam bashir musa
Dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah, mai shekara 29, zai iya komawa wata kungiyar kwallon kafa ta Ingila a kakar wasa mai zuwa idan ba a kulla sabuwar yarjejeniya tsakaninsa da kungiyar ba. (The Athletic – subscription required)
Dan wasan gaba na Senegal da Liverpool Sadio Mane mai shekara 30 zai bar kungiyar a karshe wannan kakar wasan, inda ake sa ran zai koma Bayern Munich. (Fabrizio Romano, Twitter)
Kungiyar Chelsea ta fara tattaunawa da Sevilla kan sayo Jules Kounde, kan fam miliyan 50. Dan wasan mai shekara 23 ya taimakawa kungiyarsa lashe gasar Europa a 2020. (Sport – in Spanish)
Newcastle na tattaunawa da Hugo Ekitike, dan wasan Reims da Faransa mai shekara 19 kan fam miliyan 25. (Daily Mail’s Craig Hope, Twitter)
Manchester United na tattaunawa da Barcelona kan dauko Frenkie de Jong, dan wasan tsakiya mai shekara 25 kan fam miliyan 72.5. (Fabrizio Romano, Twitter)
Sai dai United za ta duba yiwuwar dauko Sergey Milinkovic, dan wasan tsakiya mai shekara 27 daga Lazio idan ba ta sami sayo De Jong ba. (GiveMeSport)
Juventus na da karfin gwuiwa cewa za ta mayar da Paul Pogba kungiyar. Dan wasan kasar Faransar mai shekara 29 zai bar Manchester United bayan da kwantiraginsa ta ta kare a wannan kakar wasan. (90min)
Kungiyar Wolves na daf da sayo Joao Palhinha dan wasan tsakiya Sporting Lisbon da Portugal mai shekara 26, kan fam 20m. (Sun)
Manchester City na ci gaba da bayyana sha’awar daukan Kalvin Phillips, dan wasan tsakiya na Leeds United. (Sun)
