Connect with us

News

Duk mako ana arangama tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindiga a Abuja’

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

Hukumar babban birnin tarayyar Najeriya Abuja ta ce a kusan kowane mako a kan samun arangama tsakanin jami’an tsaro da ƴan bindiga musamman masu garkuwa a wani yanki na birnin tarayya.

Ministan Birnin Tarayyar Muhammad Musa Bello wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a yau a Abuja, yace saidai jami’an tsaron na samun nasara akansu saboda akwai su isassu kuma cikin Shirin ko-ta-kwana.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan da rundunar ƴansandan birnin da jami’anta tare da hadin gwiwar wasu mafarautan sun yi nasarar fatattakar ƴan fashin daji daga wata maɓoyarsu a yankin Kuje.

A cewar ministan na yanki birnin Abuja, ƴan bindigar galibi waɗanda ake fatattaka ne a maƙwabtan jihohi kasancewar yankin na zagaye da jihoji masu fama da matsalar tsaro.

Sai dai ya ce kafin su yi nasarar kai hari sau ɗaya sai jami’an tsaro sun farke layar hare-harensu da dama.

Sai dai kodayake ya ce akwai isassun jami’an tsaro da za su iya kare birnin da sauran garuruwan da ke zagaye da shi,ba za su iya samun cikakkiyar nasara ba sai da haɗin kan mazaunansa.

Advertisement

A lamarin na baya-bayan nan dai rundunar ƴa nsandan yankin na birnin Abuja ta ce jami’anta sun yi arangama da ƴan fashin daji a wata maɓoyarsu da ke yankin Kuje shekaran jiya Talata, inda har suka kuɓutar da mutum huɗu da suka yi garkuwa da su.

Sai dai ɗaya daga cikin mafarautanta suke taimaka wa ƴansandanya rasa ransa a arangamar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending