News
Fashewar tukunyar gas ta jikkata mutum 20, da ƙona shaguna a Kano
Daga maryam bashir musa
Ko a cikin watan da ya gabata sai da aka samu irin wanna fashewa da ta yi sanadin rayuka tara a KanoImage caption: Ko a cikin watan da ya gabata sai da aka samu irin wanna fashewa da ta yi sanadin rayuka tara a Kano
An samu fashewa a shagon sayar da gas ɗin girki a wata unguwa da ke cikin garin Kano, lamarin da ya jikkata mutum 20 da ƙona shaguna da dama.
Wannan na zuwa ne makwanni bayan samun shigen wannan fashewar a titin Aba ta kasuwar Sabon Gari a Kano, inda mutum 9 da suka mutu baya ga wadanda suka jikkata.
Ko da yake a wannan lokacin an yi ta samun bayanai masu cin karo da juna, rundunar ‘yan sanda na cewa tukunyar gas ce, ganau kuma na cewa bam ne.
Rahotanni dai na cewa iftila’in na wannan lokaci ya faru ne a unguwar Sheka, Karshen-Kwalta.
Kuma babu bayanai da aka samu na mutuwa.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
