News
Tinubu da Atiku sun fara laluben waɗanda za su mu su mataimaka
Daga Kabiru basiru fulatan
Ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, sun shiga laluben mutanen da za su yi musu mataimaka a zaben 2023.
Kakakin ganganmin yakin neman zaben Tinubu, Mr Bayo Onanuga, ya shaidawa manema labarai cewa, ɗan takarar a jam’iyyar APC zai gana da gwamnoni domin tantace mutumin da zai masa mataimaki.
Sannan kuma zuwa karshen mako ana saran, Tinubu zai gana da shugabanni jam’iyya, ciki harda sanata Abdullahi Adamu.
Yayinda Tinubu ke laluben mataimaki, shi ma Atiku dan takarar jam’iyyar adawa ya gudanar da tattaunawar sirri da gwamnonin PDP a Abuja a kokarin neman wanda zai masa mataimaki shi ma.
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
