News
Gwamnatin Jihar Kano ta ce sam ba za ta sabu ba ace Jiragen “AZMAN” ne za su yi jigilar maniyyatan jihar zuwa kasa mai tsarki.
Daga yasir sani Abdullah
Shugaban hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce hukumar ba ta san dalilin da ya sa hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta ware jirgin AZMAN AIR a matsayin wanda zai yi jigilar maniyyatan Kano zuwa Kasar Saudi Arebiya ba duk da cewa sun sha korafin cewa basa son hakan ya kasance.
Ya kara da cewa jirgin AZMAN basu da cikakkun jirage da isassun kayayyaki da za su iya kwashe maniyyatan Jihar Kano..
Tun farko dai hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta sanya hannun yarjejeniya ce da kamfanonin jiragen sama guda uku
Kamfanonin sune:MAX AIR, AZMAN da kuma wani kamfani daga kasar Saudi Arebiya mai suna FLYNAX.
