Connect with us

News

Na Shirya Mutuwa Domin Jin Dadin ‘Yan Nijeriya, Cewar Mejo Hamza Almustapha 

Published

on

Mejo Hamza Almustapha 

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar A’A a zaben 2023, Manjo Hamza Al-Mustapha ya ce a shirye ya ke ya mutu don Nijeriya da yan Nijeriya.

Hatsarin mota ya kashe mutum 18 a kan titin Legas zuwa Ibadan

Advertisement

Tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels Television.

 

Hamza Al-Mustapha ya ce fatarsa shine ya zama shugaban Nijeriya kuma ya amsa kirar ne saboda magoya bayansa daga kudu da arewa sun matsa akan dole ya fito.

 

Hamza Al-Mustapha, wanda shine dan takarar neman mulkin Nijeriya na jam’iyyar Action Alliance, AA, a zaben 2023 ya ce a shirye ya ke ya sadaukar da rayuwarsa don Nijeriya da walwalar yan Nijeriya.

 

Advertisement

Majiyar mu ta labarta mana cewa Manjo Hamza Al Mustapha ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a yayin hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television.

 

Majiyar tamu ta labarta mana cewa Al Mustapha yace wannan karon ya sake amsa kiran yan Nijeriya da dama, manya da yara daga Arewa zuwa Kudu da kungiyoyi da dama.

 

Kiran ya zo ne daf da lokacin mika fom din takara ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta. “Mun zauna kun kalli wasu jam’iyyun, mun zabi wanda akidunmu suka zo daya muka gano Action Alliance na da abin da muke bukata. Mun shiga Action Alliance kuma muna ta aiki ta karkashin kasa tun bayan gangamin taro. Muna aiki tukuru,” wani sashi cikin jawabinsa.

 

Advertisement

Al-Mustapha ya ce fatansa shine ya zama shugaban Nijeriya kuma ayyukan da ya yi a baya sun isa zama hujja a kansa ga yan Nijeriya.

 

Na yi aiki a wurare da dama kafin in zama soja. Na yi abin da ba za ka iya fahimta ba cikin gaggawa, musamman yi wa Nijeriya hidima. Abin da muka yi a soja hujja ne.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending