Connect with us

News

Ganduje Ya Amince da Tallafin Miliyan 33 Ga Daliban Da Suka kammala Digiri A Kasar Faransa

Published

on

Ganduje

Daga mujahid danlami garba 

 

 

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince tare da bayar da tallafin Naira Miliyan Talatin da Uku 33 a matsayin alawus alawus ga Malaman Jihar Kano da ke ci gaba da karatun digiri daban-daban a kasar Faransa.

Na Shirya Mutuwa Domin Jin Dadin ‘Yan Nijeriya, Cewar Mejo Hamza Almustapha 

Cikin wata sanarwa da kwamishiniyar ilimi mai zurfi, Dakta Mariya Mahmoud Bunkure, ta fitar a ranar Lahadin nan, ta ce kudaden na daya daga cikin kudaden da ake kashewa a karkashin shirin ” *Faransa – Gwamnatin Jihar Kano”*.

Advertisement

Idan dai za a iya tunawa, a ci gaba da kokarin da gwamnati ke yi na inganta ilimi da kuma inganta harkokin ilimi a jihar, gwamnan a madadin jihar ya rattaba hannu da gwamnatin kasar Faransa kan yarjejeniyar horar da Malamai daga Kano a jami’o’in Faransa,’’. Sanarwar ta ce.

 

‘’Wadannan malaman suna cikin manyan jami’o’i masu daraja a duniya masu sha’awar Kimiyya da Fasaha ta musamman. ”

 

Sanarwar ta ce ta hanyar wannan tsari, daruruwan malamai da aka zabo daga manyan makarantun jihar sun kammala kuma sun sami digiri na biyu da na uku. Wasu da dama suna kan matakin karshe na kammal karatunsu.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending