Connect with us

News

Hatsarin mota ya kashe mutum 18 a kan titin Legas zuwa Ibadan

Published

on

Hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

Mutum aƙalla 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan na Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya, kamar yadda hukumomi suka bayyana ranar Lahadi.

Peter Obi ya gargaɗi magoya bayansa kan maja da Kwankwaso

Advertisement

Mai magana da yauwn hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa a Najeriya, Bisi Kazeem, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 10:20 na dare a ranar Asabar a kusa da Gadar Isara, inda hatsarin ya ritsa da mutum 25.

 

Mista Kazeem ya ƙara da cewa gudun wuce kima da kuma karya ƙa’idojin tuƙi ne suka haddasa hatsarin da ya jawo mutuwar mutanen.

 

Mutum shida daga cikin 25 ɗin maza ne, da mace ɗaya, sai kuma yaro namiji ɗaya. Sai dai kuma ba a iya tantance sauran mutum 17 ba.

 

Advertisement

Karo da motocin suka yi ya haifar da fashewa da tashin gobara, inda ya ƙunshi motoci uku, a cewar sanarwar da Mista Kazeem ya saka wa hannu.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending