Connect with us

News

Ƴan vigilante sun cafke matasa da su kankware wajen satar awaki a

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAH

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Rundunar tsaro ta ƴan vigilante a jihar Kano ta ce ta samu nasarar kama wasu matasa uku da suke yawo cikin unguwanni suna satar kayayyakin al’umma bayan sun saci wata akuya.

Advertisement

 

Aminiya ta tawaito cewa dubun matasan ta cika ne a kan titin gidan gona dake tsakanin unguwar Dandinshe da kuma wani ɓangare na Kurnar Asabe da ke Karamar Hukumar Dala a cikin birnin Kano.

Advertisement

Kano ta fi kowacce jiha yawan karɓar katin zaɓe — INEC

Matasan, da aka bayyana sunansu da Usman da Bilal da Abba, sun fada hannun jami’an na bijilanti ne karkashin jagorancin Mataimakin Kwamandan Rundunar ta Jihar Kano, DC Danlami Akibu.

Advertisement

 

Danlami ya ce, “Matasan suna yawo a babur din Adaidata Sahu kuma suna dauke da makami wajen tsorata mutane su kuma kwace musu kaya.”

Advertisement

 

Yayin da aka yi bajekolinsu dai sun amsa dukkan laifukan da ake zarginsu da aikatawa kuma sun ce ba wannan ne karo na farko da suke wannan laifi ba.

Advertisement

 

Sai dai sun bayyana nadamarsu tare da cewa ba za su kara aikata hakan ba a nan gaba.

Advertisement

 

Mataimakin Kwamandan bijilantin ya kara da cewar da zarar sun kammala bincike za su mika wadanda ake zargin ga Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano domin ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending