Connect with us

Sports

Everton na son sake dauko Gueye, Marseille na tattaunawa da Milan kan Sanchez

Published

on

Idrissa Gueye

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Everton ta yi wa Paris St-Germain magana kan kokarin sake dauko dan wasan tsakiya na Senegal Idrissa Gueye, ana sa ran ci gaba da tattaunawa nan da kwanaki kadan masu zuwa. (Fabrizio Romano)

Advertisement

 

Za a yi wa Nuno Tavares gwajin lafiya a Marseille ranar Juma’a, bayan da kungiyar mai buga wasa a Faransa ta cimma matsaya kan daukar dan wasan na Portugal a matsayin aro daga Arsenal. (Fabrizio Romano)

Advertisement

MDD ta buƙaci Poland ta daina nuna wa ‘yan Afirka masu neman mafaka wariya

Marseille din ta kuma fara tattaunawa a kokarin ta na dauko dan wasan gaba na Chile Alexis Sanchez, mai shekaru 33, daga Inter Milan. (L’Equipe – in French)

Advertisement

 

Ita kuwa West Ham tana ci gaba da tattaunawa da Eintracht Frankfurt a yunkurinta na sayen dan wasa Filip Kostic, mai shekara 29, wanda ke iya buga gaba ko baya ta bangaren hagu. (90min)

Advertisement

 

Tottenham za ta yi kokarin shan gaban Juventus a yunkurin dauko dan wasan gaba na Italiya Nicolo Zaniolo, mai shekara 23, daga Roma. (Tuttosport – in Italian)

Advertisement

 

Barcelona ta nuna sha’awarta ta sayen dan wasan Tottenham Sergio Reguilon, mai shekaru 25, matukar ta kasa dauko takwaransa na Sifaniya Marcos Alonso, mai shekara 31, daga Chelsea. (AS – in Spanish)

Advertisement

 

 

Advertisement

AC Milan ta cimma yarjejeniya da Club Bruges kan sayo Charles de Ketelaere, duk da cewa Leeds da Leicester sun nuna sha’awar daukar dan wasan, dan asalin kasar Belgium. (90min)

 

Advertisement

Palmeiras ta ki amincewa da tayi har sau biyu daga Ajax kan sayen matashin dan wasan Brazil na gaba Giovani, yanzu haka kuma wasu kungiyoyin biyu, wato Newcastle da Bayer Leverkusen su ma sun nuna suna son sayen dan wasan. (ESPN – in Portuguese)

 

Advertisement

Dan wasan baya na Newcastle United da Ingila Kieran Trippier, mai shekaru 31, ya ce kiris ya rage ya tafi Manchester United a bara, kafin daga baya ya zabi tafiya Newcastle daga tsohuwar kungiyarsa ta Atletico Madrid a watan January. (Mirror)

 

Advertisement

Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta bai yi amfani da mai tsaron raga Bernd Leno, mai shekara 30, da ‘yan wasan baya Pablo Mari, da Haector Bellerin ba a wasan da kungiyar ta sha kashi hannun Brentford. Kuma ana kyautata zaton ‘yan wasan uku za su bar Emirates cikin wannan kaka mai kamawa. (Mirror)

 

Advertisement

Everton na shirin karbar nata kason kudin na cinikin dan wasan Najeriya mai shekaru 24 Ademola Lookman, wanda Atalanta ta amince ta saye daga RB Leipzig kan kudi yuro miliyan 15. (Sky Sport Italia – in Italian)

 

Advertisement

Mai horas da ‘yan wasan Liverpool Jurgen Klopp ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewar dan wasan gaba na kungiyar Roberto Firmino zai iya barin kungiyar a wannan lokaci bayan da wasu bayanai ke alakanta dan wasan da kungiyoyin Juventus da Newcastle. (90min)

 

Advertisement

Tottenham na iya sayar da Giovani lo Celso matukar aka amince za a biya ta kudi kimanin fam miliyan 17, bayan da kungiyoyin Villarreal da Fiorentina suka nuna sha’awar sayen dan wasan tsakiyar dan asalin kasar Argentina. (Athletic – subscription required)

 

Advertisement

Manchester City ta nuna alamun cewa za ta iya kyale James McAtee, mai shekara 19, dan asalin kasar Ingila ya tafi wata kungiya a matsayin aro a wannan kakar, inda ake alakanta dan wasan da kungiyoyin Leeds United da Nottingham Forest. (Football Insider)

 

Advertisement

Leicester City ta yi rashin nasara a takarar da take yi da Napoli wajen dauko dan wasan tsakiya dan asalin kasar Koriya ta Kudu, Kim Min-jae daga Fenerbahce saboda karancin kudin cefane. (Football Insider)

 

Advertisement

Burnley ta mika tayin ta ga kungiyar Club Bruges ta Belgium a kokarin sayen dan wasan tsakiya dan asali kasar Scotland Jack Hendry. (Mail)

 

Advertisement

 

BBC

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending