Connect with us

Sports

Ronaldo Zai Fafatawa Portugal Wasa A Euro Na Shakarar 2024

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Cristiano Ronaldo na daf da buga babbar gasar tamaula ta duniya ta 11 jimilla, bayan da aka bayyana shi cikin wadanda za su buga wa tawagar Euro 2024.

Advertisement

Mai shekara 39, mai taka leda a Al-Nassr ta Saudi Arabia, shi ne kan gaba a yawan buga wa kasar wasanni a tarihi, wanda ya ci ƙwallo 128 a wasa 206.

Chelsea Da Mauricio Pochettino Sun Raba Gari

Kociya, Roberto Martinez ya saka Ronaldo cikin ƴan kwallo bakwai masu cin ƙwallo cikin 26 da zai je da su babbar gasar tamaula ta nahiyar Turai da za a yi a Jamus.

Advertisement

Ronaldo ya fara buga wa tawagar gasar Euro 2004 lokacin da kasar ta kai wasan karshe da ta karbi bakunci, amma ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Girka.

Wanda ya lashe Ballon d’Or biyar ya taimakawa Portugal ta ɗauki Euro 2016 – shi ne babban kofin da ya dauka na kasa da kasa – da kuma Nations League a 2018/19.

Advertisement

Ƴan wasa tara ne daga cikin tawagar da suke buga Premier League a cikin tawagar da Martinez ya bayyana da suka hada da ƴan kwallon Wolves uku, wato Jose Sa da Nelson Semedo da kuma Pedro Neto.

Sauran daga cikin masu buga Premier League sun hada da ɗan wasan Manchester United, Bruno Fernandes da Diogo Dalot da na Manchester City, Bernardo Silva da kuma Ruben Dias.

Advertisement

Sauran sun hada da na Fulham, Joao Palhinha da kuma na Liverpool, Diogo Jota.

Haka kuma Martinez zai je Euro 2024 da dattijo, Pepe mai shekara 41 tare da matashi mai shekara 21 dake taka leda a Porto, Francisco Conceicao.

Advertisement

Conceicao, mai taka leda daga gefen gaba ɗan gidan Sergio tsohon dan wasan tawagar Portugal, ya fara buga wa kasar tamaula a karawa da Slovenia cikin Maris.

Portugal za ta kara da Jamhuriyar Czech a rukuni na shida a wasan farko ranar 18 ga watan Yuni daga nan ta yi gumurzu da Turkiya da Georgia.

Advertisement

Ƴan wasan tawagar Portugal da za su buga Euro 2024

Masu tsaron raga: Diogo Costa (Porto), Jose Sa (Wolves), Rui Patricio (AS Roma)

Advertisement

Masu tsaron baya: Antonio Silva (Benfica), Danilo Pereira (Paris St Germain), Diogo Dalot (Manchester United), Goncalo Inacio (Sporting), Joao Cancelo (Barcelona), Nelson Semedo (Wolves), Nuno Mendes (PSG), Pepe (Porto), Ruben Dias (Manchester City)

Masu buga tsakiya: Bruno Fernandes (Manchester United), Joao Neves (Benfica), Joao Palhinha (Fulham), Otavio Monteiro (Al Nassr), Ruben Neves (Al-Hilal), Vitinha (PSG)

Advertisement

Masu cin ƙwallaye: Bernardo Silva (Manchester City), Cristiano Ronaldo (Al Nassr), Diogo Jota (Liverpool), Francisco Conceicao (Porto), Goncalo Ramos (PSG), Joao Felix (Barcelona), Pedro Neto (Wolves), Rafael Leao (AC Milan).

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending