Uncategorized
Chelsea ta sayi dan wasan gaban Portugal Diego Moreira mai shekaru 18 daga Benfica
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Chelsea ta tabbatar da daukar matashin dan wasan Portugal Diego Moreira mai shekaru 18 daga Benfica.
Moreira ya koma Benfica daga Standard Liege a shekarar 2020 kuma yana cikin kungiyar da ta lashe Gasar Matasa ta UEFA ta 2022.
Tsohon dan wasan Chelsea,Barcelona da Arsenal ya yi ritaya daga kwallon kafa
Dan wasan na kasar Portugal ya fara buga wasansa na farko a watan Mayun 2022, Moreira yana buga wasa akai-akai a kungiyar Benfica B a kakar wasan data gabata.
Matashin dan wasan gefe yana cikin tawagar Portugal a gasar cin kofin nahiyar Turai na ‘yan kasa da shekara 21, inda za su kara da Ingila a wasan kusa da na karshe a ranar Litinin (AEST).
Zuwan Moreira a kyauta ya biyo bayan siyan yan wasan gaba Nicolas Jackson daga Villarreal da Christopher Nkunku daga RB Leipzig, yayin da Ruben Loftus-Cheek ya kammala komawa AC Milan na dindindin.
Tafiyar Loftus-Cheek na daya daga cikin ‘yan wasan da suka fice a baya-bayan nan yayin da sabon kocin Blues Mauricio Pochettino ke sake fasalin ‘yan wasansa gabanin fara kakar wasa ta bana.
Arsenal ta kammala siyan dan wasan tsakiya Kai Havertz, yayin da N’Golo Kante da Kalidou Koulibaly da mai tsaron gida Edouard Mendy suka nufi kasar Saudiyya.
Shima dan wasan tsakiya Mason Mount yana shirin tafiya bayan Manchester United ta amince ta sayi dan wasan na Ingila kan kudi na farko na fam miliyan 55 (dala miliyan 108).
