Sports
Newcastle za ta raba Werner da Chelsea, Azpilicueta da Alonso za su koma Barcelona Timo Werner
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Newcastle United na tattaunawa da Chelsea kan daukar aron Timo Werner, dan wasan gaba mai shekara 26, wanda tsohuwar kungiyar RB Leipzig ma ke son sake sayen sa. (Sunday Mirror)
Brighton ba za ta sake tattaunawa da Manchester City kan Marc Cucurella, dan wasan baya mai shekara 24 ba kan sayar da shi, sai dai in City ta yi tayin da bai gaza fam miliyan 50 ba. (Athletic – subscription required)
Leicester City na bukatar fiye da fam miliyan 50 idan za su amince su sayar da James Maddison ga Newcastle United wadanda tayinsu na fam miliyan 40 bai sami karbuwa ba. (Times – subscription required)
Newcastle ta tuntubi Burnley kan yiwuwar sayen Maxwel Cornet amma ba ta mika tayinta kan dan wasan gefen mai shekara 25 dan kasar Ivory Coast ba. (90 Min)
Ba mu ba Tinubu, Peter Obi za mu yi – Kungiyar Afenifere
Chelsea na daf da kulla yarjejeniyar da za ta sa gola Kepa Arrizabalaga zai koma Napoli ta Italiya a matsayin dan aro na wannan kakar wasan. (Mail on Sunday)
Barcelona kuwa na son sayo ‘yan wasan baya Cesar Azpilicueta mai shekara 32 da Marcos Alonso mai shekara 31 daga Chelsea nan da makon gobe. (Sport – in Spanish)
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce yana bukatar sabbin ‘yan wasa a wannan kakar wasan, kuma Gunners sun ci gaba da mayar da hankali kan Youri Tielemans, dan wasan tsakiya na Leicester City kuma dan kasar Belgium mai shekara 25. (90 Min)
AC Milan ta amince ta dauko Charles de Ketelaere dan wasan tsakiya mai shekara 21 daga Club Bruges kan fam miliyan 26.9. An ce Leeds United ma na nemansa. (Calciomercato – in Italian)
Nordi Mukiele, dan wasan Faransa mai shekara 24 ya ce ya ki amincewa da tayin komawa Chelsea gabanin ya amince da tayin da Paris St. Germain ta yi masa. (L’Equipe, via Metro)
Tayin da Chelsea ta yi na fam miliyan 6.7 kan Cesare Casadei, dan wasan tsakiya na Inter Milan mai shekara 19 bai sami amincewar shugabannin Milan ba. (Gazzetta – in Italian
