Connect with us

Sports

Chelsea ta fara tattaunawa da Barcelona kan De Jong, Spurs na son Udogie

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Chelsea ta fara tattaunawa da Barcelona kan batun daukar dan wasan tsakiya na Netherlands, mai shekara 25, Frenkie de Jong, wanda ake ta rade-radin cewa Manchester United zai tafi. (Athletic – subscription required)

De Jong zai fi son ya tafi Chelsea a maimakon Manchester United. (Metro)

Advertisement

Chelsea na shirye ta biya dan wasan baya na Faransa Wesley Fofana albashin £200,000 a duk mako idan ta cimma yarjejeniya da Leicester City, wadda ke neman a biya ta £85m kafin a dauki dan wasan mai shekara 21. (Mail)

Manchester United ta fara tattaunawa da RB Salzburg a kokarinta na dauko dan wasan gaba, dan asalin kasar Slovenian, mai shekara 19, Benjamin Sesko. (Sky Sports)

Advertisement

Ita ma Chelsea ta tattauna da dillalin dan wasan Benjamin Sesko. (Fabrizio Romano)

Bournemouth na gab da kammala sayo mai tsaron raga na Barcelona, dan asalin kasar Brazil, mai shekara 33, Neto. (Telegraph – subscription required)

Advertisement

Tottenham ta fara tattaunawa da Udinese domin dauko dan wasan baya na Italiya Destiny Udogie, mai shekara 19, sannan akwai yiwuwar za ta sake mika wa Udinese din dan wasan a matsayin aro. (Fabrizio Romano)

Mai tsaron raga na Ingila Dean Henderson, mai shekara 25, ba zai kara buga wa Manchester United wasa ba, bayan da ya tafi Nottingham Forest a matsayin aro, kamar yadda tsohon dan wasan tsakiya na Tottenham, Jamie O’Hara ya bayyana. (Talksport) 

Advertisement

Mai tsaron baya na Chelsea, dan asalin kasar Ingila, Levi Colwill, mai shekaru 19, na shirin tafiya Brighton, yayin da dan wasan baya na Brighton din Marc Cucurella, mai shekara 24, ke gab da komawa Chelsea. (football.london)

Dan wasan gefe na Croatia, Ivan Perisic, mai shekara 33, ya nemi shawarar abokin wasansa, tsohon dan wasan Tottenham, Luka Modric kafin yanke shawarar barin Inter Milan zuwa kungiyar da ke wasa a birnin London. (Mirror)

Advertisement

Kungiyoyi da dama da ke buga gasar kungiyoyin kwallon kafar Ingila ta biyu (Championship) da ta uku (League One) ne suka nuna sha’awar daukar dan wasan tsakiya na Manchester United, dan asalin kasar Wales, Charlie Savage, mai shekara 19, a matsayin aro. (Mail)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending