News
Ban taba bakin ciki ko nadama don an cire ni daga sarkin Kano ba — Sanusi II
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammad Sanusi II, yace bai taba bakin ciki don an cire shi daga sarkin Kano ba, domin tuni Allah yayi masa jagoranci a rayuwarsa, don haka godiya zaiyi ga Allah ba bakin ciki ko nadama ba.
“A shekarar da ta gabata na cika shekaru 61, na zama shugaba a bankin UBA da First Bank, na zama gwamnan babban bankin Nigeria, na zama sarkin Kano, na zama Khalifan Tijjaniyya, idan har nayi bakin ciki ban kasance mai godiya ba, domin wasu dama daya suke neman cikin damammakin dana samu, amma basu samu ba.”
Najeriya Ta Tabarbare Fiye Da Yadda Take A 2015 – Sunusi
Sanusi II yayi kaurin suna wajen bayyana abinda yake ganin gaskiya akan kowa, domin a cewarsa ya gwammace ya rasa duk mukaminsa akan gaskiya, wanda kuma a watan Maris din shekarar 2020 ne gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta warware rawaninsa na sarkin Kano, bisa zargin rashin bawa gwamnatin goyon baya.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
