News
NDLEA ta kama tsohon soja da zargin sayar wa ‘yan fashin daji ƙwayoyi a Sokoto
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani tsohon soja mai shekara 90 da zargin yi wa ‘yan fashin daji safarar ƙwayoyi a Jihar Sokoto.
Wata sanarwa ta ce an kama Usman Adamu ne ranar Laraba, 3 ga watan Agusta a garin Mailalle na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni.
Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa ta bude shafinta ga masu son koyan habbaka fasaha.
“An kama shi da tabar wiwi mai nauyin 5.1kg,” a cewar kakakin NDLEA Femi Babafemi.
Kazalika a ranar Alhamis, hukumar ta kama wata mota a JIhar Zamfara maƙare da ƙwayar Diazepam 50,000 a kan hanyarta ta zuwa Sokoto daga birnin Benin na Jihar Edo, wanda ta ce mallakar wani ne mai suna Umaru Attahiru.
A wani binciken na daban, NDLEA ta damƙe wani fasto mai suna Anietie Okon Effiong da duro uku na ƙwayar crystal methampetamine – wadda ake kira Mkpuru Mmiri a Najeriya.
Kayan da NDLEA ke zargin an shiga da su ne daga Indiya, an kama su yayin da ake shirin kai su wani wuri a birnin Legas lokacin da aka tare motar da ke ɗauke da su.
BBC NEWS
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
