Connect with us

News

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa ta bude shafinta ga masu son koyan habbaka fasaha.

Published

on

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa ta bude shafinta ga masu son koyan habbaka fasaha.

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

 

 

Advertisement

Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Kasa (NITDA) ta bukaci ‘yan Najeriya da su nemi shirin horas da su kan bunkasa manhajoji (NITDA Developers Group, NDG) da suke jira.

 

 

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa hukumar ta ce shirin a karkashin kulawar ma’aikatar sadarwa ta tarayya da tattalin arziki na zamani na daga cikin kokarin ganin Najeriya ta zama cibiyar fasahar zamani a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.

 

Hukumar NITDA ta sanar da shirin horar da masu samar da manhaja miliyan daya a fannoni daban-daban na bunkasa aikace-aikace.

Advertisement

Wainar Da Aka Toya A Makon Farko Na Firimiyar Ingila Ta Bana

Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wata sanarwa da shugabar harkokin kasuwanci da hulda da kasashen waje NITDA, Misis Hadiza Umar ta fitar a ranar Asabar din nan, ta ce aikin wanda za a gudanar da shi ta hannun reshen NITDA, National Center for Artificial Intelligence and Robotics (NCAIR) da ke gundumar Wuye, a Abuja, na hadin gwiwa ne da masu ruwa da tsaki a cikin yanayin muhalli.

 

An karanta cewa: “Shirin ya yi daidai da National Digital Economy Policy and Strategy (NDEPS) wato manufofin tattalin arziki na zamani da Dabaru na Ƙasa na Gwamnatin tarayya, da kuma NITDA’s Strategic Road Map and Action Plan (SRAP 2021-2024) ginshiƙin habbaka Fasaha.

 

“Masu horon za su bi ta cikin jerin koyarwa, da laccoci don haɓaka ƙwarewar shirye-shirye a kan Python don Intelligence Artificial, Injin Learning, Blockchain, Robotics da Kimiyyar Bayanai.

Advertisement

 

ADVERTISEMENT

“Babban Darakta na NITDA, Kashifu Inuwa, CCIE, ya umurci NCAIR da ta gudanar da shirin a karkashin tsarin aiki na 24/7 a cikin Cibiyar, gami da shirin horarwa wanda zai ba da horo mai zurfi ga matasan Najeriya da nufin samar da masu haɓaka software.

 

“Koyarwar NDG ta kasu kashi biyu (A&B). Batch A zai gudana daga Litinin zuwa Laraba, Batch B zai gudana daga Alhamis zuwa Asabar, Lahadi kuma za ta kasance ranar karatu mai zaman kanta, kuma za a ba da takaddun shaida ga ɗalibai da masu horarwa a ƙarshen shirin.”

 

Advertisement

(SOLACEBASE)

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending