Connect with us

News

Shugaban PDP Na Zamfara, Sani Ahmad, Ya Rasu

Published

on

Dokta Sani Ahmad

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara, Dokta Sani Ahmad, ya rasu.

 

Advertisement

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Sauya fasalin naira – EFCC ta nemi taimakon bankuna da ‘yan canji don kama masu laifi

Advertisement

 

Mataimakin Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Mukhtar Lugga ne ya tabbatar da rasuwar marigayin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Gusau, babban birnin jihar, ta wayar salula.

Advertisement

 

Lugga ya ce rashin lafiyar da ta yi ajalin marigayin takaitacciya ce, saboda ko a ranar da zai rasu, sai da ya gana da Majalisar Malamai ta Jihar a Gusau.

Advertisement

 

Ya ce an tabbatar da rasuwar marigayin ne bayan da aka dauke shi zuwa asibiti bayan da jikinsa ya yi zafi.

Advertisement

 

Marigayin ya rasu yana da shekara 62, kuma ya bar mata biyu da ‘ya’ya shida.

Advertisement

 

A ranar 23 ga watan Satumba aka zabi marigayin a matsayin shugaban PDP na Zamfara bayan murabus da Kanal Bala Mande ya yi

Advertisement

 

(NAN)

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending